ƙa'idojin Murad a Hausa
Bayan bayanai masu mahimmanci da shawarwari da aka samu a duniya yayin rubuta ka'idar Murad, an kammala nazari mai zurfi da gyare-gyare. Wannan tsarin gyara ya jawo mutane masu tsira da sauran masana cikin rubuce-rubucen bita da bita kan daftarin gyare-gyare. Wannan ya kawo nau'in 'sigar aiki' na tsairin ƙa'idojin Murad,wanda aka saki a ranar sha uku watan Afrilu 2022. Cikakken taken Ka'idojin shine “Ka'idojin tattara bayanai da kuma amfani da su akan Keta haddin/ko cin zarafin dan adam”.
An bayar da ita Fassarar ‘sigar aiki’ na Ka’idojin Murad a cikin Hausa a kasa. Ka’idojin takarda ce wacce za a sake duba ta lokaci-lokaci don tabbatar da cewa ta ci gaba da nuna mafi ƙarancin ƙa'idodi don amintaccen, inganci da tattara bayanai game da SCRSV.